RAHA A WASU WAQOQIN ALIYU NAMANGI

  • : Ms Word, Ms Word Format
  • : 78 Pages
  • : ₦3,000 | $25 | ₵60 | Ksh 2720
  • : 1-5 Chapters
  •  
  • Click to DOWNLOAD Materials

RAHA A WASU WAQOQIN ALIYU NAMANGI

Abstract:

This research work titled “Raha a wasu waqoqin Aliyu Namangi” (Comedy in some of Aliyu Namangi’s poems) comprises of explanations of how the Artist used comedic expressions in some of his poems. The work also made some criticisms on the kinds of comedic statements he used in the poems to entertain the people. At the end of the study, it was discovered that Aliyu Namangi used these statements in his poems in order to strengthen the relationship that exists between him and his relatives even though the poems were spiritual in nature

QUMSHIYA

Declaration                 –           –           –           –           –           –           –           –           ii

Certification –              –           –           –           –           –           –           –           –           iii

Dedication       –           –           –           –           –           –           –           –           –           iv

Godiya –          –           –           –           –           –           –           –           –           –           v

Tsakure           –           –           –           –           –           –           –           –           –           vii

Abstract           –           –           –           –           –           –           –           –           –           viii

Qumshiya        –           –           –           –           –           –           –           –           –           ix

BABI NA XAYA

SHIMFIXA

1.0       Gabatarwa       –           –           –           –           –           –           –           –           1

1.1    Taqaitaccen Tarihin Aliyu Namangi     –           –           –           –           –           1

1.1.1 Karance-Karancensa –                –           –           –           –           –           –           2

1.1.2  Aikace-Aikacensa         –           –           –           –           –           –           –           4

1.2       Dalilan Bincike           –           –           –           –           –           –           –           9

1.3      Manufar Bincike          –           –           –           –           –           –           –           10

1.4       Muhimmancin Bincike           –           –           –           –           –           –           10

1.5       Hasashen Bincike        –           –           –           –           –           –           –           11

1.6       Iyakacin Bincike         –           –           –           –           –           –           –           14

1.7       Naxewa           –           –           –           –           –           –           –           –           12

BABI NA BIYU: WAIWAYEN AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0       Gabatarwa       –           –           –           –           –           –           –           –           13

2.1       Ma’anar Raha –           –           –           –           –           –           –           –           13

2.2        Ire-Iren Raha –            –           –           –           –           –           –           –           14

2.3       Raha a Rayuwar Bahaushe     –           –           –           –           –           –           16

2.3.1  Raha a Adabin Bakan Bahaushe           –           –           –           –           –           17

2.3.2    Raha a Rubutaccen Adabin Bahaushe            –           –           –           –           24

2.3.2.1 Raha a Qagaggun Labarai na Hausa –             –           –           –           –           25

2.3.2.2 Raha a Rubutattun Wasannin Kwaikwayo na Hausa –           –           –           27

2.3.2.3 Raha a Rubutattun Waqoqin Hausa –              –           –           –           –           29

2.4 Ayyukan Da Suka Gudana Kan Aliyu Namangi –            –           –           –           30

2.4.1 Kundaye –           –           –           –           –           –           –           –           –           30

2.4.2 Littattafai            –           –           –           –           –           –           –           –           34

2.4.3 Muqalu –             –           –           –           –           –           –           –           –           36

2.5 Ayyukan da suka Gudana kan Raha         –           –           –           –           –           38

2.5.1 Kundaye –           –           –           –           –           –           –           –           –           38

2.5.2 Littattafai            –           –           –           –           –           –           –           –           42

2.6       Ayyukan da Suka Gudana Kan Rubutattun Waqoqin Hausa –           –           43

2.7.1    Kundaye          –           –           –           –           –           –           –           –           43

2.7.2    Littattafai         –           –           –           –           –           –           –           –           48

2.7.3 Muqalu –             –           –           –           –           –           –           –           –           53

2.8       Naxewa           –           –           –           –           –           –           –           –           59

BABI NA UKU

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

3.0       Gabatarwa       –           –           –           –           –           –           –           –           60

3.1       Xakunan Karatu          –           –           –           –           –           –           –           60

3.2        Ziyara –           –           –           –           –           –           –           –           –           61

3.3       Ganawa/Hira da Wasu Mutane-          –           –           –           –           –           61

3.3.1     Hira da Malam Umar –           –           –           –           –           –           –           62

3.3.2    Hira Da Murtala Namangi      –           –           –           –           –           –           63

3.4        Ra’in Bincike –           –           –           –           –           –           –           –           64

3.5         Kammalawa –            –           –           –           –           –           –           –           65

 

BABI NA HUXU

RAHA A WASU WAQOQIN ALIYU NAMANGI

4.0       Gabatarwa       –           –           –           –           –           –           –           –           66

4.1       Raha Barkwai a Wasu waqoqin Aliyu Namangi        –           –           –           66

4.2        Raha Faxi-in-faxa a wasu Waqoqin Aliyu Namangi –           –           –           76

4.3       Raha Shaguvau a Wasu Waqoqin Aliyu Namangi     –           –           –           80

4.3.1    Raha Shaguvau Mai Sigar Wa’azi a Wasu Waqoqin Aliyu Namangi           84

4.4       Kammalawa – –           –           –           –           –           –           –           89 BABI NA BIYAR: KAMMALAWA

NAXEWA

5.0       Gabatarwa –     –           –           –           –           –           –           –           –           90

5.1        Kammalawa  –            –           –           –           –           –           –           –           90

5.2       Shawarwari     –           –           –           –           –           –           –           –           91

5.3       Naxewa           –           –           –           –           –           –           –           –           92

Manazarta Ratayen Wasu Waqoqin Aliyu Namangi

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA XAYA SHIMFIXA

1.0    Gabatarwa

Marubuta waqoqin Hausa wasu mutane ne da Allah (S.W.T) ya ba su wata baiwa da hikima da fasaha ga kuma basira wajen shirya waqoqin Hausa a rubuce, domin isar da wasu saqonni masu muhimmanci ga al’umma. Haka kuma sukan shirya waqa su kuma tsara ta a kan abubuwa daban-daban waxanda suka shafi rayuwar jama’a.

Har wa yau kuma kusan kowanne marubuci da irin hanya ko salon da yakan bi wajen tsara waqarsa, duk da cewa mafiya yawa daga marubuta waqoqin

Hausa sukan rubuta waqoqinsu ne bisa jigon wa’azi da gargaxi da tarbiyya ko

faxakarwa.

Haka kuma wani lokaci marubuta waqoqin Hausa kan yi amfani da wasu zavavvun kalmomi ko wasu zantuka na musamman a waqoqinsu domin samar da raha ko sanya nishaxi a zukatan jama’a saboda hakan zai haifar da rashin gundura

ga mai karatu ko sauraron waqoqin Aliyu Namangi.

Aliyu Namangi na xaya daga cikin ire-iren waxannan marubuta waqoqin Hausa wanda ya yi amfani da wasu zavavvun zantuka na raha a wasu waqoqinsa, a inda wannan bincike zai gudana a kansu domin gano ire-iren rahar da ya yi amfani da su a waxannan waqoqin nasa da ake hasashen cewa suna qunshe da zantuka na raha a cikinsu.

                1.1       Taqaitaccen Tarihin Aliyu Namangi

 Fagen nazari na tarihin rayuwa da ayyukan marubuta waqoqin Hausa, fage ne mai faxi wanda masana da manazarta suka jima suna binciko tarihin xaixaikun marubuta waqoqin Hausa da ayyukansu, domin bayar da gudummuwa tare da bunqasa wannan fage na adabin rubutacciyar waqa.

Masana da manazarta da dama sun kawo tarihin Aliyu Namangi a aikaceaikacensu da suka gudanar, ire-iren waxannan ayyuka na manazarta kan Aliyu

Namangi sun haxa da Skinner (1969) da Xangambo (1973) da Hassan (1973) da Birniwa (1989) da Yakawada (1987) da Sankalawa (2005) da Muhammad (2010) da Muhammad (2011) da Nazifi (2011). Dukkansu sun bayyana cewa an haifi Aliyu Namangi ne a wani qauye mai suna Mangi a kusa da birnin Zariya. Hijira na da shekara dubu xaya da xari uku da goma sha biyar (1315) A.H. wacce ta yi dai-dai da shekara ta dubu xaya da xari takwas da casa’in da huxu (1894) A.D. A

ranar Larabgana wato Larabar qarshen watan safar, wato watan biyu na Musulunci.

An kuma haife shi ne a lokacin sarkin Zazzau Kwasau, sunan mahaifinsa Ishaq, sunan mahaifiyarsa kuwa Hauwa’u. An haifi Aliyu Namangi lafiyarsa qalau kamar sauran jarirai. Bayan shekara xaya da haihuwarsa a watan safar sai idanunsa suka tsiyaye a sakamakon rubdugun cutar ‘qyanda’ da ta ‘Agana’ da suka same shi a lokaci xaya. Wannan shi ne musabbabin makancewar Aliyu Namangi, kuma an yi masa kaciya yana da shekara bakwai da haihuwa.

(Yakawada, 1987:6-8).

1.1.1 Karance-Karancensa

 Bayan an yi wa Aliyu Namangi kaciya ya warke sai mahaifinsa ya danqa shi a hannun wani malami mai suna malam Ibrahim domin ya karantar da shi

Alqur’ani mai girma. Fara karatunsa ke da wuya sai malam Ibrahim ya yi qaura daga garin Mangi, sai aka mayar da shi wurin malam Gambo, a wurinsa ne, ya yi karatun Alqur’ani har zuwa izu huxu. A lokacin da malam Gambo ya tashi yin qaura daga garin Mangi zuwa cikin birnin Zariya bai bar Aliyu Namangi a baya ba, tare suka tafi (Muhammad 2010: 57-58).

Bayan da Aliyu Namangi ya kai shekara goma sha shida da haihuwa sai mahaifinsa ya yi masa kyautar wata baiwa. Da ya kai shekara ashirin da xaya, sai mahaifinsa ya yi masa auren fari. Duk da larurar ido da kuma auren da aka yi masa, bai hana shi neman ilimi ba. Ba kamar sauran xalibai masu gani ba Aliyu Namangi haddace karatunsa  kullum yake yi sai ya kawo haddarsa kafin a xora masa wani sabon karatun. Duk da cewa ba ya gani shi ma ana rubuta masa ne a allo kamar sauran xalibai. Idan ya mance da karatunsa, sai qaninsa Abdulqadir ya tuna masa, idan ya duba allonsa. (Muhammad (2011:30-32)

Aliyu Namangi bai tsaya a kan karatun Alqur’ani kaxai ba, ya yi karatun wasu fannoni na ilimi a wajen malamai da dama. Daga cikin littattafan da ya karanta akwai Qawa’idi da Ahlari da Ishimawi da Iziyya da Risala da Askari da muhutasar da tafsiri da sauran littattafan addini.

Neman ilimin Aliyu Namangi ba wai kawai a Mangi ya tsaya ba ya yi tafiye-tafiye da dama domin neman ilimi wurin malamai daban-daban kamar irin su malam Muhammadu Gwandu da malam Na’iya Zariya, da malam Ramalan Limamin Wushishi, da malam Yahuza Zariya, da Malam Sa’idu Kusfa Zariya, da malam Na’ta’ala Wusono, da malam Abdulqadir Banufe, da dai sauransu.

Bayan waxannan malaman waxanda suka taka rawa a rayuwar Aliyu

Namangi ta fannin ilimi, sai Shitawa (zuriyar Shitu xan Abdurra’uf). Domin shi da kansa ga abin da yake cewa a waxannan baitoci na waqarsa ta “Imfiraji” juzu’i na biyu.

Ni da Shitawa na saba,

Tun gaban ban hankali ba,

Sun riqe ni, riqon da ba, Duka xa a kai ma shi ba,

 Im ba gatansa tai yawa ba.

 

Shaihuna Abdurra’ufi,

Tun ina yaro la’ifi,

Ya riqe ni riqon nazifi, Har ya zam na fara qarfi,

 Bai bar ni cikin hakukuwa ba.

 

Shi ya ce min “kai karantu”,

Ko da ba ka gane ka wadatu,

Dubi Tahamisin Tafattu”

 Sai ban ji rabo kamar sani ba.

(Yakawada, 1987:7-8)

1.1.2 Aikace-Aikacensa

 Duk da cewa Aliyu Namangi ya karanci littattafai na addini da na waqoqi kamar su Alburda wacce Busari ya rubuta, da Ishiriniyar da Alfazazi ya rubuta da dai sauran littattafai na waqoqi waxanda ba Aliyu Namangi kawai suka qarfafa wa gwiwar wallafa waqoqi ba, har ma da sauran tsofaffin marubuta waqoqi musamman ma masu jihadi. Waxannan littattafai da waqoqin Madahu sun burge Aliyu Namangi. Amma kuma bai tava tunanin rubuta waqa ba, sai da ya ji waqar “Jiddul Ajizi” Ba’ajamiya, ta malam Shitu Xan Abdurra’uf daga bakin abokin bararsa mai suna malam Lawal Xan Limamin Jaji malam Adamu. Shi malam

Lawal ba makaho ba ne, amma saboda almajiranci yake bara da Aliyu Namangi. Daga nan sai ya roqi Allah da ya ba shi fasahar iya tsara waqa, wacce ta yi kama da ta malam Shitu xan Abdurra’uf. Bayan da Allah maxaukakin Sarki ya hore wa

Aliyu Namangi fasahar iya tsara waqa, sai ya fara rubuta tasa waqa wacce ya raxa mata suna Kanzil Azimi (Babbar Taska) wannan waqa tana da baiti dubu biyu, amma waxanda aka iya samu a yanzu su ne dubu xaya da xari shida da hamsin da biyu (1652). Kuma ita ce waqarsa ta farko. Har wayau, ta qunshi jigon wa’azi da madahu. A sashen wa’azi kashin waqar na farko yana cewa:

  • Mu san Ta’ala xai na mu tabbatu,

Sarki ne da buwaya da girmansa Jalla mai iko.

  • Komai yai hani da shi ba ta kansa ke nan,

Mu tsarci abin da yai hani, in muka bar shi ma ga alhairi.

A kuma sashen waqar kashi na biyu, wato na yabon Annabi (SAW) sai ya ce:

  • Allah ka buxe basiran sani garan

In yabi Annabinka Sidi Muhamman bisa hali goma

 

  • Lizimci wannan suna da ambato

Ko washe kai nufin yabo nasa lada dubu ake ba ka,

 

(1112)Yabo Sayyidil munji ko a ko’ana

Kowashe ka faxo ma’aikin Allah ba ka yi savo ba.

Daga nan kuma ya qara yin wata waqar wacce ita ce waqarsa ta biyu, ya yi ne domin yabon Annabi (S.A.W) mai suna “Tarjimul Shariri” (wato jifan shaixan). A inda yake cewa:

Bismillahi zan fara da waqa, Arrahmani Summar Rahimi,

 

Mai kotso da Baraga da Jauje, Kowa na yabon hakimainai.

                                     

Ni da na xinka gangar yabona,

                                                Sai na nufe ka Hairal bariya,

 

Annabi ya fi sauran halitta,

                                                Ba fikon savi ko taqa ba.

                                                                        (Yakawada, 1987:8-9)

Kamar yadda aka gani, waqoqin da aka ba da misali da su duk ba su da amsa-amo, amma waqarsa ta uku ita ce waqa ta farko da ya fara yi wa amsa-amo.

Wannan waqa kuwa ita ce, waqar ‘Imfiraji’ ya yi wannan waqa ce sakamakon roqon da aka yi masa da ya shirya waqar da muryar waqar caji’, ta yabon Manzon

Allah (S.A.W.) wacce ta yi wannan roqon ita ce ‘yarsa ta fari mai suna Hauwa, wacce take auren Limamin Gargai a wancan lokacin. A bisa al’adar Bahaushe akwai kunya tsakanin xan fari da mahaifansa. A sakamakon haka, sai ta shaida wa kishiyarta mai suna Ajuji. Da jin haka, sai Ajuji ta tafi ta shaida wa Aliyu

Namangi buqatar da Hauwa take da shi. Da ya tashi biya wa ‘yarsa wannan buqata tata, sai ya yi kara irin ta mutanen da, bai ambaci sunan ‘yarsa ba a matsayin wacce take da buqatar, sai ya ambaci sunan kishiyarta Ajuji wacce aka aika. Hakan ya tabbata a cikin waqar a baiti na 67 inda yake cewa:

Wanga talifi da na ji,

Waqe-waqen masu caji,

Nai ma ‘yata ce Ajuji,

Sai na sa mata Imfiraji,

            Mai yin ta ba zai baqin ciki ba. 

 

                                                                         (Yakawada, 1987:9-10)

Waqar da ke bi wa ‘Imfiraji’ ita ce waqar “Katifa” wacce ya samo karinta daga wasu Bare-bari da suka zo Zariya suna yin wata “waqar Kwambilo” ya yi wannan waqar ce saboda buqatar da matarsa ta yi masa da ya yi waqar. Ga yadda ya fara waqar Katifa

Allah, Ta’ala ka ban

Waqar da ta zan daban

Da tasu, domin yabon Maxaukaki, shugaban

         Duka, sayyadil Ambiya.

 

Ya Arrahmar Rahimi, Na, qara so da’imi

Ga musxafal ka’imi,

Muhammadu Hashimi,

         Mai magani don wuya 

                                 (Yakawada, 1987:9-10)

 

Haka kuma ya yi wata waqa mai suna ‘waqar ‘Nafisa’, ta yabon Annabi (S.A.W) ya kuma faxi sunan waqar a baitin qarshe inda yake cewa:

Ga waqa Nafisa,

Nakan ji Lawal da Isa,

Sukan ta wajen Wusasa

A ce Gude na da Hausa,

            Da sai ta iya ta tsira.

(Yakawada, 1987:10-11)

 

Daga nan kuma sai ya wallafa “waqar Basukur” a shekarar (1959) ya yi wannan waqa ta “Basukur” ce, a lokacin bukin samun mulkin kan Arewa. A wannan lokaci ne aka buqaci mawaqan baka da marubuta da su shirya waqoqi, don murnar bukin. An ba su damar yin waqar da suke so dangane da zuwan Turawa qasar Hausa da samun mulkin kai saboda haka sai Aliyu Namangi ya tsara wannan waqa ta “Basukur”, inda yake cewa:

Muna shukura ga Rabbal Alamina  Da Alherin da yai mana ba kaxan ba,

 

Muna murna da mulkin Ingilishi

Zuwad da suka yi qasarmu ba tai tsiya ba.

 

Zama zamaninsu ne aka zo da faifa, Kuxi ba masu nauyaya aljihu ba.

                                                                                    (Yakawada, 1987:11-13)

 Baya ga waqar Basukur, sai waqar Kuntigin shaixan. Ita wannan waqa an yi ta ne da nufin yi wa jama’a gargaxi, da su bar aikata laifi suna cewa shaixan ne ya yaudare su, domin kuwa ranar lahira shaixan zai qaryata zargin da suke masa, kuma ya kaxa molonsa yana yi wa ‘yan wuta dariya yana cewa:

Aha yayyayye aha iya,  Ursatu ku bar zargi na,

 

Da an muku doka kun qi ji,

Ku kai aiki mummuna

 

 

Aka sa ku ibada kun qiya

Halinku ya zam tamkana

 

Ana sallah da subahi  ku yi naku da rana.

                                                            (Yakawada, 1987:13-14)

 Daga wannan waqa kuma sai waqar Qazama, domin wa’azi ga jama’a game da auren mata Qazamai da su kansu mata Qazamai da su daina qazanta, inda yake cewa:

Ya Allahu, Rabbana, taimake mu,

Mu gargaxi ‘yan’uwa da auren Qazama.

 

Auren tsohuwa hasara ga yaro,

Gwammaci tsohuwa ga auren Qazama.

 

In ba ka san ta ne ba kau tambaye ni, In Allah ya yarda ka san Qazama.

 

Mummunan halin Qazama na fari, Ba ta fyace majina sai da dama.

                                    (Yakawada, 1987: 14-15)

 

Baya ga waxannan waqoqi da aka bayyana a baya, Aliyu Namangi ya wallafa wasu waqoqi da dama waxanda ke da jigo dabam-dabam. Waxannan waqoqi sun haxa da:

Waqar Qahon Karo

Waqar Irshadil Qulubi

Waqar Fasalu ma Yadibu fi haqqihi Ta’ala

Waqar Fasalu ma Yastahihu fi haqqihi Ta’ala

Waqar ma Yajibu Shukura fi haqqihi Ta’ala

Waqar Ma Yakunu fi haqqihi Ta’ala

Waqar ma Yajuzu fi haqqihi Ta’ala

Aliyu Namangi ya samu Digirin girmamawa daga Jami’ar Ahmadu Bello

da ke Zariya a fannin rubuce-rubucen waqoqin Hausa a ranar 2 ga watan Disamba shekara ta alif xari tara da saba’in da takwas (1978). A wurin wannan biki ne, ya rera wata waqa mai suna waqar Murnar Samun Digirin Girmamawa.

A qarshe Aliyu Namangi ya rasu a ranar 27-4-1994. A lokacin yana da shekara xari da biyu (102). Shekara xari a kalandar Nasara. Amma wajen shekara xari da biyu a kalandar Musulunci.

Aliyu Namangi ya haifi ‘ya’ya 64 a Duniya, amma ya rasu ya bar ‘ya’ya (21) maza goma sha huxu mata bakwai (7) matan aure guda (4). An haife shi ranar Laraba ya rasu ranar Laraba. Allah ya jiqansa da Rahamarsa, amin.

(Yakawada 1987:15-16)

                1.2       Dalilin Bincike

Duk da cewa an gudanar da bincike-bincike game da raha wasu kuma dangane da ire-iren gudummuwar da Aliyu Namangi ya bayar wajen havaka rayuwar al’ummar Hausawa ta fuskar addinin Musulunci, ta hanyar wa’azantarwa da faxakarwa a cikin waqa. Sa’annan kuma an san Aliyu Namangi a matsayin

malami kuma mai waqoqi kan wa’azi da madahu.

  • Amma sai ga shi raha na xaya daga cikin salailan da suka yi fice a waqoqinsa, saboda haka wannan bincike zai bincika ya gano hikimarsa ta yin amfani da wannan salo na raha a waqoqinsa.
  • Haka kuma an lura da cewa manazarta sun gudanar da aikace-aikace da dama kan raha amma mafiya yawa daga cikinsu sun fi karkata ga qagaggun labarai da tatsuniyoyi da kuma wasannin kwaikwayo na Hausa. (iii)Wata hujjar kuma ita ce an zavi gudanar da binciken ne a kan wasu waqoqin Aliyu Namangi masu qunshe da zantuka na raha a cikin su. Domin an bincika an ga cewa akwai qarancin bincike game da ire-iren waxannan waqoqi masu qunshe da zantuka na raha.

 

                1.3       Manufar Bincike

Haqiqa babu wani bincike da za a gudanar ba tare da wata manufa ba. Saboda haka, yana daga cikin manufar gudanar da wannan bincike:

  • Gano hikimar Aliyu Namangi wajen yin amfani da salon raha a waqoqinsa.
  • Qara tabbatar da cewa zantuka na raha na da muhimmanci ga al’umma saboda baya ga haifar da nishaxi, wata hanya ce mafi sauqi wajen isar da saqo ga jama’a.
  • Bin diddigin hasashen da ake ganin cewa a duk lokacin da aka ji wasu zantuka na raha za a taras da cewa wani abu ne da ya shafi wasa, babu gaskiya a tattare da shi.
  • Har wa yau kuma za a yi qoqari a gano shin mece ce hikimar mawallafin ta yin amfani da ire-iren waxannan zantuka na raha a waxannan waqoqi da ya wallafa?

                1.4       Muhimmancin Bincike

Waqa muhimmiyar hanya ce ta isar da saqo ga al’umma, kuma hanya ce da za a iya fahimtar tunani da fasahar mutum ga kuma sanya nishaxi a tsakanin al’umma. Saboda haka yana da matuqar muhimmanci a gudanar da wannan bincike a wasu waqoqin Aliyu Namangi masu qunshe da zantuka na raha a cikin

su.

  • Domin zai qara zaburar da ‘yan’uwa manazarta da su qara zage damtse wajen gudanar da bincike kan nazartar raha a wasu rubutattun waqoqin Hausa da ma na baka.
  • Haka kuma binciken yana da muhimmanci domin za a yi qoqarin fito da baitocin da suke qunshe da zantuka na raha daga waqoqin da aka nazarta, sannan kuma a taskance su a matsayin wani aiki na adabin (rubutattun waqoqin Hausa), kuma su zama masu alfanu ga sauran manazarta.
  • Har wa yau ana fata wannan bincike ya zamo fitila ga sauran marubuta waqoqin Hausa ta yin amfani da irin wannan salo na zantuka na raha a lokacin da suke rubuta waqoqinsu saboda samar da nishaxi ga masu karatu ko sauraron waqoqin domin gudun gundura da waqoqin.

1.5   Hasashen Bincike

An lura da cewa akwai qarancin bincike game da abubuwan da suka shafi raha a rubutattun waqoqin Hausa. Saboda haka, yana daga cikin hasashen da suka haifar da wannan bincike, wato domin a gano:

  • Matsayin raha a idon Bahaushe
  • Yadda al’ummar Hausawa suke kallon duk mutumin da suke amfani da zantuka na raha a wallafarsa.
  • Matsayi ko jigon waxannan waqoqi masu qunshe da zantuka na raha a

cikinsu.

                1.6       Iyakacin Bincike

Hausawa kan ce komai na da iyaka, amma ban da ikon Allah, domin haka ya zama wajibi ga duk wani mai gudanar da bincike a kan wani batu a san iyakar da’irar ko farfajiyar da bincikensa zai gudana.

Manazarta kan yi hakan ne, domin kauce wa cin karo da wani aiki da ya yi daidai ko kama da nasu domin gudun kar a maimaita aikin da wani ya gudanar.

Hakan zai samar da aiki ingantacce kuma karvavve wanda jama’a za su amfana da wasu abubuwan da ba su san da su ba. Saboda haka, an taqaita wannan bincike ne a kan wasu waqoqin Aliyu Namangi da ake hasashen cewa suna qunshe da zantuka na raha a cikin su.

Waqoqin kuwa su ne (i) waqar Basukur (ii) waqar Zambon Qazama (iii) waqar Kuntigin Shaixan (iv) waqar Tambihu Anami (faxakar da jama’a).

A taqaice dai waxannan waqoqi guda huxu su ne aiki zai duba domin nazartar ire-iren zantuttukan raha da ke cikin su.

                1.7       Naxewa

Tun a farkon wannan babi aka kawo shimfixa wacce ta gabatar da yadda za a gudanar da wannan bincike inda aka yi taqaitaccen bayani kan yadda marubuta waqoqin Hausa ke tsara waqoqinsu, haka kuma an yi bakandamiyar shimfixa da ta shafi kusan dukkan abubuwan da za a duba a lokacin gudanar da wannan bincike.

Bayan nan an kawo dalilan bincike wato abubuwan da suka haddasa gudanar da wannan bincike, sai manufar bincike wato makomar wannan bincike idan ya kammala, sannan kuma sai aka bayyana muhimmancin binciken wato irin gudummuwar da binciken zai bayar musamman ma a wannan fage na ilimi.

Daga nan kuma sai aka tantance hanyoyin da aka bi wajen gudanar da binciken da iyakar binciken mai nuna inda da’irar binciken za ta tsaya.

 

RAHA A WASU WAQOQIN ALIYU NAMANGI

Sharing is caring!

Leave a Reply